//
Friday, April 3

An kama malamin Firame da yayi wa dalibinshi mai shekaru 8 ta’adin fyade a Bauchi

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

A jihar Bauchi a arewacin Najeriya, an zargi wani malamin makarantar Firamare, Haruna Aliyu, mai shekaru 45 yi wa wani dalibinshi mai shekaru 8 luwadi.

An zargin malamin da ba’a bayyana sunanshi ba da baiwa yaro N10 domin yin lalata dashi, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

DABO FM ta tattara cewa tini dai rundunar ‘yan sandan jihar ta cafke malamin ta kuma mikashi gaban Kotu domin karbar hukunci.

‘Yan sandan sun kama malamin ne bayan yaron ya fara rashin lafiya wanda daga haka ne iyayenshi suna samu labarin abinda ya faru.

Jami’in ‘yan sandan da ya gurfarnar da mutumin, Insfecta Yusuf Usman yace a ranar 6 ga watan Disambar bara, wani mazaunin unguwar Ganjuwa ta cikin garin Bauchi, ya shigar da korafin wani Haruna Aliyu yayi luwadi da ‘danshi a ofishin ‘yan sanda.

Masu Alaƙa  Katsina: 'Yar shekara 14 ta yanke gaban magidancin da yayi yunkurin yi mata fyade

Insfectan yace mahaifin yaro yace mutumin da ake zargin ya kai yaron cikin dakinshi ya kuma aikata aikin cin zarafin luwadi. Bayan aike malamin zuwa kotun Majistire dake cikin garin Bauchi, ‘dan sanda mai kara ya roki Kotu ta bashi lokacin kara tattara shaidu akan laifin wanda ake zargi, abinda kotun ta amince.

Kotu ta aike malamin, Haruna Aliyu zuwa gidan gyaran hari domin zaman wucin gadi tare da dage cigaba da zaman shari’ar zuwa ranar 7 ga watan Fabarairun 2020.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020