Mai girma gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da tabbacin daukar mataki akan gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, bayan ya ruguje Masallaci.
Gwamnan ya bayyana haka ta hannun mataimakinshi a fanni Labarai, Abba Anwar.
“Munyi mamaki matuka a lokacin da muka samu labarin. Ina tabbatarwa da mutane cewa, zamuyi duk mai yiwuwa wajen daukar mataki na kin amincewa rushe Masallacin daga hukumomin da suka dace.”
“Wannan al’amarin bazai wuce ba har sai mun kaishi ga hukumomi domin yin abinda ya dace.”
Ganduje, yayi kira ga mutane dasu kwantar da hankulansu, su cigaba da tabbatar da zaman lafiya tare da yin kasuwancinsu domin tini gwamnati ta fara yunkurin daukar mataki akan rushe Masallacin.
