Labarai

Uba ya kashe ‘danshi mai shekaru 3 kacal a jihar Kano

A garin Gaya dake jihar Kano, wani magidanci ya hallaka dan da ya haifa ta hanyar sanya masa Shinkafar Bera.

Magidancin mai suna Musbahu, ya amsa tabbacin shine wanda ya hallaka dan nashi bisa kasancewar ya samu dan ba ta hanyar aure ba.

A zantawar magidancin da gidan Rediyon Freedom dake jihar Kano ya bayyana cewa ya kashe dan nashi mai shekaru uku kacal a duniya bisa rashin mahaifiyar da zata reneshi tare da kuma kasancewar ya sameshi ba ta hanyar aure ba.

DABO FM ta tattaro magidanci yana mai neman sassauci a sa’ilin da za’a yanke masa hukunci.

Da yake tabbatar da al’amarin, kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, DSP Haruna Abdullahi ya ce hukumar tana kammala bincikenta zata aikeshi gaban kuliya domin karbar hukunci.

Karin Labarai

UA-131299779-2