Labarai Siyasa

Bana cikin taron hadin kan APC na ‘Babba-da-Jaka’ da Yari ya kira -Sanata Marafa

Jigo a jam’iyyar APC ta jihar Zamfara, Sanata Kabir Marafa ya nesanta kansa daga taron ‘yan takarkarun gwamna na jihar wato G-8, wanda Abdulaziz Yari ya kira.

Rahotan Dabo FM ya bayyana cewa wannan ya biyo bayan wata sanarwa da sakataren Jam’iyyar APC ta tsagin Abdulazeez Yari, Shehu Isa ya fitar.

Sanarwar tace Yari ya hada ‘yan takarkarun gwamna na jihar Zamfara domin kawo karshen rigingimu na jam’iyyar a jihar kamar yadda DailyNigerian ta wallafa.

Sanata Marafa ya bayyana cewa: “Babu wanda ya tuntube ni da sunan tattaunawar kawo karshen rigingimu na jam’iyyar APC.” Taron da ya bayyana da taron babba da jaka.

“Ai [Yari] yama toshe duk wata hanya da zamu hadu mu kawo karshen wannan rigingimu kamar yadda uwar jam’iyya ta kasa ta bada umarni.”

Marafa ya dora da cewa, “Ni halin yanzu ina goyon bayan duk wata hanya da zata kawo karshen matsalar tsaro data addabe mu wadda sabuwar gwamnatin jihar Zamfara keyi.”

“Zanci gaba da hada kai da wannan sabuwar gwamnatin domin samun dauwamammen zaman lafiya a jihar Zamfara.”

Karin Labarai

Masu Alaka

El-Rufa’i yayi tir da kashe Tiriliyan 17 a gyaran wutar lantarki da gwamnatin Buhari tayi

Muhammad Isma’il Makama

Zamfara: Gishirin Lalle yayi sanadiyar mutuwar mutum 14

Muhammad Isma’il Makama

A kalla ‘Yan Gudun Hijira 25,000 suka koma Gidajensu na ainahi a jihar Zamfara

Dabo Online

Zamfara: Jami’an tsaro basa mana aikin komai – Sarkin Shanun Shinkafi

Dangalan Muhammad Aliyu

Sarkin Zurmi na Zamfara ne yace a kashe dukkan mutanen Dumburum – Gov Abdul’aziz Yari

Dangalan Muhammad Aliyu

Zaben Gwamna: Kotu ta umarci INEC ta cire sunan dan takarar gwamnan APC a jihar Akwa Ibom

UA-131299779-2