//
Tuesday, April 7

Hanyar Kaduna zuwa Abuja tafi kowacce hanya tsaro a duk fadin Najeriya -El Rufai

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Gwamnan jihar Kaduna, Mal Nasiru El-Rufai ya bayyana cewa, a yanzu haka duk fadin Najeriya babu babbar haya da ke da tsaron hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Dabo FM ta jiyo gwamnan yana bayyana hakan ne bayan ya bude wani taro na hukumomin tsara da ake gudanarwa a jihar kamar yadda DailyTrust ta bayyana.

Ya kuma bayyana cewa, an kwashe watanni biyu da rabi ba’a samu labarin yin garkuwa da wani a kan wannan hanyar ba saboda matakai da gwamnati ke ci gaba da dauka.

El-Rufai ya bayyana cewa: “Hanyar Kaduna zuwa Abuja a yanzu ta fi kowacce hanya tsaro a Najeriya a yanzu saboda jiragen sama na sojojin sama da ke aiki a wannan hanya suna samar da bayanai.”

Masu Alaƙa  Yadda Hakimin Birnin Gwari ya tsere daga hannun masu garkuwa da mutane suna tsaka da barci

Sai dai kuma ya kara da cewa: “Amma har yanzu mutane na jin tsoron bin wannan hanya.”

“A yanzu kusan duk masu garkuwa da mutane da ke gefen hanyar duk an tarwatsa su ko kuma an kora su cikin jeji,” in ji shi.

Ya ce, ko da yake ana ci gaba da yin garkuwa da mutane a jihar amma bai yi muni kamar yadda ake yi a baya ba.

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020