Malama Halima Shittu, uwargidan Sheikh Abdulwahab, malamin addinin Islama dake jihar Kano, ta rasu yau Talata 5 ga watan Ramadana.
Iyalan malamin ne suka sanar da haka da safiyar yau.
Za a yi jana’izarta kamar yadda addinin musulunci ta tanada a gidan malamin dake unguwar Sharada Phase II dake birnin jihar Kano.
Kafin rasuwar ta taba rike kwamandar hukumar Hisbah sashin Mata a hukumar dake jihar Kano.