Kiwon Lafiya

Mutane sama da miliyan 3 ne suka kamu da Koronabairas a fadin duniya

Adadin yawan mutanen da suka kamu da cutar Kwabid-19 ya zarta miliyan 3 fadin duniya inda kasar Amurka ta zama kasar da ta bi kowacce kasa yawan masu dauke a cutar a duniya.

Cikin kiduduggar da jami’ar John Hopkins ta kasar Amurka ta fitar, tace zuwa yanzu sama da mutane miliyan 3 da dubu uku da doriya ne cutar ta kama a duniya tare da hallaka mutane sama da dubu 209,300.

Cutar da ta fara tsamari daga birnin Wuhan a kasar Sin ta yanjo tsayuwar dukkanin al’amuran da aka saba yi na yau da kullin a fadin duniya cikin walwala.

DABO FM ta tattara cewar; bisa kiduddugar jami’ar ta Hopkins, mutane sama da dubu 55 cutar ta hallaka a kasar Amurka wacce itace ke kan gaba a fadin duniya. Kasar Italiya tana biye mata baya da mutuwar mutane sama da 26,000. A kasar Andalus kuwa cutar tayi sanadin mutuwar mutane sama da dubu 26.

Zuwa yanzu a nahiyar Afrika cutar ta bulla a kasashe sama da 50 daga cikin kasashen da suke nahiyar. Bincike na nuna cewar kasar Lesotho da Tsibirin Comoros ne cutar bata shiga ba a nahiyar Afirika.

Sai dai duk da yawan shigar cutar cikin kasashen Afrika, cutar tafi yi wa kasashen yamma illa.

Zuwa yau 28 ga watan Afrilun 2020, cutar ta kama mutane 1337 a Najeriya tare da hallaka mutane 40, an kuma samu warkewar mutane 255 daga cutar.

Karin Labarai

Masu Alaka

Yadda ake ciki game da Koronabairas a jihar Yobe

Ibraheem El-Tafseer

Yanzu yanzu: An samu karin mutane 11 masu dauke da Coronavirus, jumillar 373 a Najeriya

Dabo Online

Ganduje ya kori mota cike da ‘yan cirani zuwa Kano daga Abuja

Dabo Online

Gwamnati ba zata tallafawa wadanda suke da sama da N5000 a asusun banki ba – Sadiya Faruk

Dabo Online

Jihar Zamfara ta rufe dukkanin iyakokinta don kariyar Coronavirus

Aisha Muhammad

Yanzu yanzu: An samu karin mutum 23 masu dauke da Coronavirus, jumilla 174 a Najeriya

Dabo Online
UA-131299779-2