Ranar ashirin da biyar ga watan disambar kowacce shekara mabiya addinin kiristanci suna farin ciki a wannan rana domin muryar zagayowar ranar haihuwar Jesus.
A wannan shekarar ma bata sauya zani ba, rana ce ta farin ciki wacce ta kunshi addu’o’i, ziyara da sauran kyawawan aiyuka a wannan rana. Al’ummar kasashe daban daban mabiya addinin sun nuna farin cikin su kamar yadda suka saba, kamar yadda zaku gani a video.
Jawabin shugaban ɗarikar katoliya Paparoma Francis yayi kira ga kiristoci dasu zauna lafiya da juna kuma yayi bayanin cewa bambance-bambance da’a ake samu a duniya ba illa bane face arziki.
Daga karshe yayi kira ga shuwagabanni duniya da su ƙara maida hankali akan zaman lafiya a duniya inda ya bayyana jin dadinshi akan bayanai masu nuna tsagaita wuta a yakin kasar Yemen.