Labarai

Jihohin Kano, Katsina da Jigawa zasu fuskanci matsanancin rashin wutar Lantarki

Kamfananin dake rarraba wutar lantarki na ‘KEDCO’ ya bayyana shirinshi ya katse haske wutar lantarki a jihohin Kano, Katsina da Jigawa bisa rikakken bashin da suke bin mutane.

Shugaban gudanarwar kamfanin, Ibrahim-Shawai, ya bayyana haka ne a wata sanarwa daya mikawa kamfani dillancin labaran Najeriya ‘NAN’ a ofishin kamfanin dake jihar Kano.

“Makarantu, Kamfanunuwa da wasu gidajen yada labarai da suka hada da gidan Jaridu ne manyan wadanda muke bi bashin.”

“A sabida haka, a wani salo da zamuyi na dawo da tarin bashin da muke bi tare da cika umarnin babban kamfani rararaba hasken lantarki na kasa wajen biyan kaso 100 na kudaden wutar kowanne wata.”

Shugaban Kamfanin ya yi bayani kan cewa kamfanin ya dauki damarar gintse wutar lantarki a wuraren da suke da tulin bashin saboda masu amfani da wutar basa son su biya bashin da ake binsu na biliyoyin Nairori.

“A watan Janairu zuwa Yulin 2019 kadai, Kamfanin KEDCO ta bankado bashin Naira biliyan 10 da take bin mutane, wanda hakan ba abune mai kyau ga kowanne irin kasuwanci ba duba da cewa muma muna biya ne kafin a bamu wutar.”

Karin Labarai

Masu Alaka

Kamfanin Lantarki na KEDCO ya na bin Kanawa bashin Naira biliyan 148

Dabo Online
UA-131299779-2