//
Thursday, April 2

Gwamnatin ta sake jaddada kudurinta na fitar da ‘Yan Najeriya miliyan 100 daga talauci

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Gwamnatin Najeriya ta jaddada kudurin da ta dade tana fada na fitar da ‘yan Najeriya kimanin miliyan 100 daga matsanancin talaucin da suke fama dashi.

Ministar Kudin kasar, Zainab Ahmad, itace ta sake bayyana haka a ranar Litinin, yayin wata ganawa da tayi da gidan Talabijin na NTA.

DABO FM ta tattaro cewa ma’aikatar Kudin ta wallafa bayanin Minsitar a shafinta na Twitter.

“Shugaba Muhammadu Buhari ya umarce mu fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci, wanda kuma shine ginshikin inda muka sa gaba.

Ministar tace bisa umarnin shugaba Buhari, dole kasar tayi sauri wajen samun canjin da shugaba Buhari yake so.

Masu Alaƙa  Tsakani da Allah har yanzu ba’a fara aikin Wutar Mambila ba - Ministan Lantarki

Minsitar ta kara da cewa; “A wannan shekarar ta 2020, dole ne mu canza daga irin salon da muke bi na bin komai a sannu, mun gane cewa tsarin da muke bi yanzu bazai kai mu zuwa ga yacce shugaban kasa yake so ba.

“Shugaban kasa ya wajabta mana fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga talauci, wannan ne inda mu ministoci muka bi bawa gaba.

“Saboda haka, dole ne ya zama cewa muna samar da ayyukanyi domin rage matsalar rashin aikinyi da kuma cire mutane daga talauci.

“Shiyasa a tsarin kashe kudi da mukayi, za’a mun bada karfi sosai wajen saukaka harkokin kasuwanci ga kananan da mafi karanta yan kasuwa. Wannan shi yasa muka aminta ta wannan itace hanyar da tallatin arziki zai habaka har ma ya tsaya da kafarshi.

Masu Alaƙa  Ma'aikatar wutar lantarki ta kasa na shirin kara tsunduma yajin aiki

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020