//
Sunday, April 5

Matashi ya biyawa dalibai 44 kudin jarabawar NECO da WAEC kyauta

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Wani matashi mai kishin al’umma Alhaji Ibrahim Garba Umar Madalla, ya tallafawa matasa da biyan kudin rubuta jarabawar NECO da WAEC a karamar hukumar Zariya ta Jihar Kaduna.

Da yake tabbatar da labarin ga Dabo FM a Zariya, Ibrahim Garba Umar, ya ce wannan ba shi ne karo na farko da yake daukar nauyin dalibai ta hanyar tallafa masu a bangarori daban-daban. inda ya ce, hakan zai taimaka wurin sanya yaran akan turbar da ta dace musamman a bangaren karatun su, Kuma dalibai 44 suka ci gajiyar wannan tallafi.

Ya kara cewa, taimakon nasa ba ya tsaya ne kawai ga biyan kudin jarabawa ba, ya taimaka ma wasu wurin biyan kudin rajista a makarantun gaba da sakandare daban-daban dake fadin kasar nan.

Masu Alaƙa  Watanni biyar da daukewar tauye hakki da akayi wa matashi Abubakar Idris ‘Dadiyata’

A cewar Ibrahim Garba, taimakon matashi taimakon alumma ce baki daya, saboda su ne kashin bayan cigaban kowacce alumma.

Ya nuna bukatar da ke akwai ga zababbu a matakai daban-daban, su dukufa wurin taimakon al’umma, musamman domin rage radadin talauci da al’umma ke ciki a yau.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020