Wasu daga Sarakunan gargajiya na da hannu a rikicin arewacin Najeriya – Minista

Mansur Dan Ali, ministan tsaron Najeriya ya bayyana cewa, sabbin bayanan sirri suna nuni da cewa, wasu daga sarakunan gargajiyar Arewacin Najeriya na da hannu dumu dumu a kashe-kashen da ake fama dasu a yankunan arewar.

Ministan ya aikewa Jaridar Premium Times, inda yace sun gano daga bayanan sirri cewa wasu sarakunan gargajiya na da hannu a hare-haren ‘yan bindigar, inda ya tabbatar da cewa nan gaba kadan zasu fuskanci hukunci.

Daga karshe Ministan, ya bukaci al’ummar yankunan Katsina, Sokoto da Zamfara da sauran yankunan arewacin Najeriya su tashi tsaye wajen taimakon gwamnati domin kakkabe abinda ya addabi al’ummar wannan yankin.

Hare-haren yan bindigar dai ya tsananta a jihar Zamfara, inda a makom daya wuce aka kashe kusan mutane 43 a wani hari da ‘yan bindigar suka kai kauyukan Kurya, Kursawa da makwotansu dake karamar hukumar Shinkafi.

Masu Alaƙa  Tsaro: 'Yan bindiga sun harbe manoma 10 a Zamfara

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: