Zaben Kano: Kotu ta amince da bukatar “Abba Gida Gida”

Karatun minti 1

Kotun sauraren korafe korafen zaben gwamna a jihar Kano, ta amince da rokon da lauyoyin dan takarar gwamnan jahar Kano a jam’iyyar PDP, Engr Abba Kabir Yusuf suka yi.

Lauyoyin PDP, sun roki kotu data bawa hukumar INEC umarnin baiwa lauyoyin dukkanin takardun zaben ranar 9 da 23 ga watan Maris da aka gudanar da zaben gwamna a jihar Kano, domin zasu zame musu hujja gaban kotun.

Gidan Rediyon Dala dake jihar Kano ya rawaito cewa, kotu ta bada hukumar INEC umarnin baiwa Engr Abba Kabir Yusuf duk wasu takardu da yake bukata kamar yadda wakilinta Yusuf Nadabo Isma’il a kotun ya tabbatar.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog