Masana suka ce Soyayya ruwan zuma ce, idan aka sha sai a baiwa masoyi.
Wadansu masoya biyu daga jihar Kano sun aiko mana da sako kamar yacce aka saba bisa ga tsarin aikinmu na karbar sakonni daga masu kasancewa damu idan har an cika sharadanmu.
Sai dai sun bukaci da mu boye sunayensu.
Sun bukaci a fada duniya irin halin kunci da dimaucewar da suka shiga dalilin rashin magana tsakaninsu har na tsawon kwanaki biyar.
Saurayin ya bayyanawa DABO FM cewa rashin maganar tasu tazo ne bisa dalilin zana jarrabawa da budurwar tashi take yi a wata jami’a a jihar Kano.
Itama a nata bangaren, budurwar ta shaida mana cewa sunyi matukar kokari kuma ya kamata a yaba musu, kasancewar duk wanda ya sansu zai yi mamaki idan aka ce sun dauki tsawon wadannan kwanakin basuyi koda sallama ba.
Saurayin ya bayyana cewa shine ya bukaci haka saboda tsananin son da yake mata ne yasa ya yanke shawarar dena maganar tasu saboda ta samu nutsuwar zana jarrabawar cikin nutsuwa.
Itama budurwar ta bayyana cewa tana so ta dage ne wajen cin jarrabawar shi yasa ma taki saka wa wayar hannunta ‘Data’ domin kada ta dauke hankalinta akan karatun.
Wannan sabuwar taska ce da DABO FM ta bude domin karbar sakonni daga masoya, inda zaku iya bamu labarin soyayyarku ko kuma matsalolin da kuke fuskanta wadanda suka shafi soyayya.
Zaku iya aike mana da sakon ta shafin mu na Facebook mai sunan Dabo FM ko a adreshinmu na email ‘submit@dabofm.com’ ko ta whatsapp a lamba +918690017313.
