Home Labarai“Anyi yunwa halin kowa ya fito fili” -Nafisa, budurwar matashin da Baturiya ta biyo Kano

“Anyi yunwa halin kowa ya fito fili” -Nafisa, budurwar matashin da Baturiya ta biyo Kano

by Muhammad Isma’il Makama
0 comments

Budurwar matashin nan Sulaiman wanda Ba Amurkiya Jeanin Sanchez ta yiwo tattakin soyayya tun daga Amurka ta kuma bashi zoben kauna tare da shirin yin aure, Nafisa Tahir ta bayyana cewa ai yunwa akayi kuma halin kowa ya fito fili.

Majiyar Dabo FM ta bayyana Tsohuwar budurwar matashin ta fadi hakan ne bisa ganin yadda Sulaiman ya sauya alakarsu bayan ya hadu da baturiyar Amurka, kuma ga alama shaukin soyayyar baturiyar ya jefa shi cikin tekun kauna har takai ya mance da tsohuwar zumar sa Nafisa.

Wannan ya fito ne cikin wata tattaunawa ta baka da baka da dan jarida Nasiru Zango yayi da Nafisa, inda ta kara da cewa Umma ta gaida Ashha!

Nafisa tace sam abin bai wani dame ta sosai ba, murna ma tayi ganin cewar an yi yunwa halin kowa ya fito, dan haka tace tana yiwa Sulaiman da sabuwar masoyiyarsa fatan alheri.

Tace ta godewa Allah da Jeanine ta bayyana da wuri har takai abin boye ya fito fili.

Anasa bangaren mahaifin Sulaiman Malam Isa, yace bashi da sauran shakku akan auren dansa da sabuwar masoyiyarsa domin ya lura mutuniyar kirki ce me ladabi da biyayya, yayi musu fatan alheri a wannan aure wanda yace babu wata matsala tun da suna kaunar juna.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00