Kotu ta bayar da belin Matar da ake zargi da caccakawa Mijinta wuka

Karatun minti 1

Babbar Kotu a jihar Kano ta bayar da belin Fatima Musa, matar da ake zargi da caccakawa mijinta, Sa’eed Muhammad, wuka a ciki.

Lauya daga kungiyar kare hakkin mata mai kare Fatima Musa ce ta mika bukatar su ga kotu bisa dalilin cewa Hanan ba niyar kashe mijinta nata tayi ba.

Ta shaidawa kotu cewa tuhumar da rundunar ‘yan sanda sukeyi wa Fatima Musa na cewa ta caccakawa Mijinta wuka bata da tushe.

Tace hasalima fada ne ya kaure a tsakaninsu wanda yayi sanadiyyar zubar mata da hakwara a yayinda ita kuma ta dauki wuka ta caccaka masa don kariya.

DABO FM ta binciko cewa Kotun ta bayar da belin Fatima Musa Hanan biyo bayan rashin kalubalantar kudirin da Lauyar Hanan ta shigar daga Lauyan mai kare Sa’eed Muhammad, Barista Lamido Abba Soron Dinki.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog