“Kuna kan gwaji na wata 3” -Gov Matawalle ga sabbin Kwamishinoni da Masu Bada Shawara

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya cewa sabbin Kwamishinonin sa 19 da masu bashi shawara 28 cewa zai gwada sune na wata uku kacal.

Kafar yada labarai ta Dabo FM ta jiyo gwamnan yana bayyana haka ne a gidan gwamnatin Zamfara lokacin da yake rantsar da sabbin kwamishinoni da masu bashi shawara.

Gwamnan ya kara da cewa “Mun dora ku akan wannan gwaji na wata uku ne domin muga ko zaku iya aikin.”

“Muna fata ku tsallake wannan jarrabawa mu karasa wannan mulkin tare wanda muke fata zai samarwa da jihar mu cigaba mataki na kololuwa.”

“Sannan zamu ci gaba da duba hazakar kowannen ku sau 4 a shekara saboda ba wasa muka zo ba”

Masu Alaƙa  Matawalle ya raba Motoci ga Jami'an Tsaro da hukumar ZAROTA mai kamanceceniya da KAROTA ta Kano

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.