(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Wata mahaifiya ta jefa jaririnta cikin tsohuwar rijiya a jihar Bauchi

Karatun minti 1

‘Yan sandan jihar Bauchi sun kame wata mata bayan ta jefa jaririn da ta haife a cikinta cikin wata tsohuwar rijiya.

Bincike ya nuna cewa ta haifi jaririn ne ba bisa aure ba, kamar yadda shafin Hausa na Legit.ng ya bayyana.

DABO FM ta binciko cewa rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta hannun kakakinta, DSP Kamal Datti Abubakar ya shaidawa manema labarai cewa sun kame matar mai shekaru 23 wacce aka fi sani da Hauwa Ishaku bayan da ta jefa jaririn da ta haifa a wani kango cikin wata tsohuwar rijiya.

Hauwa wacce ‘yar asalin kauyen Bidir ce dake karamar hukumar Azare dake jihar Bauchi, ta jefa jaririn a cikin tsohuwar rijiyar da babu ruwa a cikinta.

DSP Kamal ya bayyana cewa jami’an rundunar yan sandan tayi gaggawar zuwa gurin da abin ya faru bayan da aka sanar dasu abinda Hauwa ta aikata.

Ya kara da cewa jami’an sunyi nasarar samun jaririn da ran shi, tare da yin gaggawar garzayawa dashi asibitin tarayya dake garin Azare domin karbar taimakon gaggawa hadi da yin kame Hauwa Ishiaku.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog