Ra'ayoyi

#Xenophobia: Abin kunya ne shugaba Buhari ya ziyarci kasar Afirika ta Kudu – Usman Kabara

Fitaccen dan Jarida kuma shugaba Shafin Afrika ‘POA’, Usman Ahmad Kabara, ya bayyana cewa abin kunya ne shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyara kasar Afirika ta Kudu akan kisan wariya da ake yiwa ‘yan Najeriya a kasar.

Kabara ya bayyana haka ne a shirinshi na Madubin Kabara, lokacin da yake fashin baki akan ziyarar da shugaban zai kai kasar Afirika ta Kudu.

DABO FM ta tattaro Kabara yayi nuni da cewa; wanda aka yiwa laifi, shine wanda za’a baiwa hakauri.

Ma’ana, kasar Afirika ta Kudu ce tayi wa Najeriya laifi bisa kisan ‘yan Najeriya tare yiwa dukiyoyinsu ta’adi a kasar Afirika ta Kudu.

“Shugaba Buhari yace zai je kasar Afirika ta Kudu bayan yan tawagarshi sun gana da shugaban Afrika ta Kudi, Ramaphosa. Sun nuna abinda akayi wa ‘yan Najeriya, basu ji dadinshi ba.”

“Shi kuma Muhammadu Buhari, zai je Afrika ta Kudu a watan gobe Oktoba bayan tawagar ta dawo, in ya je zai yi magana akan gyaran dangantaka tsakinin kasashen biyu da suka da babban tattalin arziki a Afirika.”

Sai dai Usman Kabara yayi tambihi irin na sukar yin gyara a game da matakin da shugaba Muhammadu Buhari ya dauka da wadanda ma yakamata ya dauka.

“Mutanen Najeriya aka kashe a Afirika ta Kudu, shin shugaban Afrika ta Kudu ne yakamata yazo Najeriya domin gyara huldar dangantakar da take tsakaninmu (Najeriya) na laifin da sukayiwa mutanen Najeriya na kashe musu ‘ya ‘ya da Jikoki?

Ko kuma kai ne(Buhari) da aka kashe maka ‘yan kasarka ne zaka tashi kaje neman meyasa aka kashe su?”

Wa yakamata yaje gyara hulda? Kai ne zakaje(Buhari) ko kuma Afirika ta Kudu ce yakamata tazo ta gyara hulda?”

Daga karshe, Kabara yayi nuni da cewa; Tin tini yakamata Buhari ya gintse wasu daga cikin kasuwancin kasar Afrika ta Kudu, korar Jakadan Kasar daga Najeriya har sai an samu sasanci tsakani.

Za’a iya kallon tallar da DABO FM bata da hurumi a kai.

Karin Labarai

Masu Alaka

Ra’ayoyi: ‘Rundunar ‘Shege-ka-fasa’ bata lokaci ne’

Hassan M. Ringim

#JusticeForKano9: Shirun ‘Yan Arewa da Malaman ‘Social Media’ akan mayarda Yaran Kano 9 Arna

Dabo Online

‘Yan siyasa na amfani da kalmar “Hassada” ko “Bakin ciki” don dakushe masu musu hamayya

Dabo Online

Meyasa wasu mutane suke jin tsoron tofa albarkcin bakinsu wajen kawo gyara a siyasa?, Daga Umar Aliyu Musa

Dabo Online

Ko dai a dawowa da Sultan alfarmarsa, ko ya zare hannunsa a komai, Daga Hassan Ringim

..

Romon Dimokradiyya: Kura da shan bugu Kato da kwace kudi, Daga Umar Aliyu Fagge

Dabo Online
UA-131299779-2