0
Kotun sauraron korafin zabubbukan Sanatoci tayi umarnin sake yin zaben zagaye a wasu mazabun jihar Osun ta Arewa a cikin kasa da kwanaki 90.
Hakan na zuwa ne bayan korafi da Sanatan PDP, Taiwo Shote, ya shigar gaban Kotu na kalubalantar nasarar Sanatan APC, Osusunya. – Sashin Hausa na Legit ya rawaito.
Kotun a karkashin mai shari’a Wakkil Alkali Gana ta soke zaben kananan hukumomin Ijebu Ode, Ijebu ta Gabas da Odogbolu.
