Labarai

Zaria: Har yanzu tsugunu bata kare ba a rikicin shugabancin karamar hukumar Zariya

Tun bayan da rikicin cikin gida ya barke a majalisar kansilolin karamar hukumar Zariya a Jihar Kaduna, yanzu haka membobi 7 daga cikin 13 na ‘yan majalisar sun amince da dakatar da shugaban majalisar Hon Hashimu Bako daga mukamin sa har na tsawon kwanaki 90 wato watanni 3.

A zaman da majalisar ta yi a safiyar Larabar nan, kansila mai wakiltar mazabar Dambo Hon Isiyaku Dalhatu, ya gabatar da kudirin da ya naimi a dakatar da shugaban majalisar saboda gaza kiran zaman majalisar kamar yadda doka ta tanada. Inda nan take kudirin ya samu goyon bayan dukkanin ‘yan majalisu 7 cikin 13 da suka halarci zaman majalisar a ranar.

Kuma suka sanya hannun amincewa da takardar tabbatar da tsigewar nan take.
Kansilolin da suka sanya hannu akan takardar dakatarwar, sun hada da Hon Aminu Sani da Hon Salisu Ibrahim da Hon Musa Salisu Imani da kuma Hon Yusha’u Muhammad.
Sauran sun hada da Hon Akilu Abubakar da Hon Isma’il Shu’aib sai kuma Hon Isiyaku Dalhatu wanda shi ne ya gabatar da kudirin.

Bayan fitowa daga zaman majalisar, sai Dabo FM ta tuntubi daya daga cikin ‘yan majalisar wanda shi ne ya gabatar da kudirin dakatar da shugaban majalisar wato Hon Isiyaku Dalhatu, inda ya bayyana mana cewar, dama tunda dokokin kananan hukumomi ya basu daman duk lokaci da aka zo gudanar da zaman majalisa, idan ba shugaban majalisa a nada wani na ruko da zai jagoranci zama.
Shi yasa su ma suka dauki wannan matakin tunda bai kaucewa doka ba, kuma yanzu haka sun tabbatar da Hon Sama’ila Shu’aibu a matsayin shugaba na riko.

A nashi tsokaci, kansila mai wakiltar mazabar Kaura Hon Salisu Ibrahim Sikifa, ya ce dukkanin zaman majalisar da akan yi a baya akan yi da shugaban majalisar, amma ta yiwu ya raina gayyatar da suka yi masa ne yasa bai samu harlartan zaman majalisar ba, amma duk da haka doka ta yi aiki a kansa kuma sun aika masa da kwafin takardar dakatar da shi.

Da Dabo FM ta tuntubi shugaban majalisar Hon Hashimu Bako ya ce, ba zai ce komai ba domin Jama’iyya ta dakatar da su daga shiga kafafen yada labarai kan rikice-rikicen shugabancin su, amma da zaran sun ji daga uwar Jama’iyya za su kira taron manema labarai.

Idan dai za’a iya tunawa, Dabo FM ta kawo maku yanda hayaniyar siyasa ta barke a karamar hukumar Zariya, wanda har ta kai ga wasu kansiloli sun yi yunkurin tsige shugaban karamar hukumar Injiniya Aliyu Idris Ibrahim daga mukamin sa, yunkurin da har yanzu bamu san inda aka kwana ba.

Karin Labarai

UA-131299779-2