Rigar ‘Yanci: Dama nasan za’a rina, tallafin Ganduje wajen ruguza Ilimin ‘yan Sakandire, Daga Nazeef Touranki

Tun lokacin da aka ce daliban zangon 2019 , baza su rubuta QUALIFYING EXAMINATIONS BA, sai sun shiga SS 3, na fahimci cewa akwai matsala.

Basu rubuta jarabawar ba sai a karshen Zangon Karatu na farko a  SS 3, duk da irin matsalolin da aka fuskanta wajen jarabawar.

Akwai Jarrabawar da sai takarda daliban suka sayo suka rubuta akai, wasu ma A4 paper aka basu suka rubuta.

Akwai jarrabawar da ko “Questions paper” ba’a kawo ba, sai a wasu wuraren aka samo, sannan akayi photocopy.

Yanzu Haka duk dalibin da zai rubuta jarabawar WAEC, shi ne ya biya wa kansa, saboda lokacin da aka fara registration din WAEC, lokacin suke rubuta J”ARRABAWAR  QUALIFYING”.

Masu Alaƙa  Hatsarin mota ya kashe mutane 9, jikkata 15 a Kano

Cikin ikon Allah sunyi dabara sun je sun biya WAEC, saboda ganin yadda Gwamnati take nuna halin ko in kula da harkar ilimin su.

Yanzu an fada musu cewa kowa zai biya naira dubu goma sha biyu (N12, 000), kudin registration na NECO, kuma ana bukatar sukai wannan kudin cikin sati daya, daga (05/04/2019 zuwa 12/04/2019).

Fitar da wannan kudi cikin sati daya a wajen Malam talaka sai a hankali, tunda Gwamnatin Jaha tayi fuska.

Yaran nan dai suna da haqqi akanku, idan kuma ba’ayi musu ba to Allah zai saka musu.

 

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Masu Alaƙa  'Yan daba sun kai hari, gidan shugaban APC na jihar Kano

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: