(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Yadda aka cashe da wakar Sunusi II ‘Sarkin Kano’ a bikin Hanan Buhari

Karatun minti 1

A tsarin da aka dauka na bikin da ake yi masa hidumar tarurruka, akan saka sauti domin jin dadin mahalarta har ma su taka su rausaya.

Bikin Hanan Buhari, ‘yar shugaba Buhari bai fita zakka kan yadda mahalarta taron suka cashe domin nuna farin ciki da bikin.

Cikin wakokin da cashe da su a wajen taron biki, akwai wakar mawakin Naziru Ahmad mai taken Mata ku dau Turame wadda ya yi wa tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II, DABO FM ta tabbatar.

A wani faifan bidiyo na taron biki da DABO FM ta gani a wajen wasu da suka halarci bikin, ya nuna yadda matan da suka halarta, da alamu sun ji dadin sanya wakar wadda ta kai su ga canza salon rawar da suke takawa.

A wani labarin kuma, mawakin nan Hamisu Breaker ya samu halartar taron bikin tare da wasu mawakan da aka gayyata.

Mawakin, Breaker ya rera wakokinsa ciki har da bakandamiyar da ake kallon ita ta kara fito da shi idan duniya, Jarumar Mata.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog