Hukumar dake kula da cututtuka ta Najeriya, NCDC ta sake tabbatar da samun karuwar masu dauke da cutar Covid-19 guda 35 a daren Alhamis.
Kamar yadda hukumar ta bayyana a shafinta na yanar gizo gizo da shafin Twitter, tace adadin wadanda aka tabbatar a Najeriya ya zama 373.
“A yau da misalin karfe 10:20 na dare an sake samun masu dauke da cutar ‘Corona Virus’ guda 35. An samu guda 19 a Lagos, 9 a Abuja, 5 a Kano da 2 a jihar Oyo.