Yadda aka gudanar da Sallar Idi a Masarautar Zazzau

dakikun karantawa

Dubban al’ummar musulmi ne suka halarci raka’oi biyu na sallar idi babba a Masallacin idi na kofar doka Zariya.

Sallar da aka fara da misalin karfe 9 na safe, bisa jagorancin babban limamin Zazzau Sheikh Dalhatu Kasimu Yero.

A cikin hudubarsa limamin na Zazzau ya hori daukacin al’ummar musulmi su koma ga Allah tare da gyara dabi’u domin samun tsira a nan duniya da gobe alkiyama.
Yace, ba za a taba samun dawwamammen zaman lafiya ba sai al’umma sun rungumi soyayyar juna da yi wa juna fatan Alheri da kuma tausayawa na kasa.

Kuma ya bukaci shuwagabanni su ji tsoron Allah yayin jagorancin su, kuma su sani Allah zai tambaye su akan dukkanin abubuwan da suka aikata na Alheri ko sharri.

Da ya juya ga mabiya kuwa, Sheikh Dalhatu Kasimu, kira ya yi gare su su cigaba da yi wa shuwagabanni addu’a tare da fatan Alheri da kuma bin umarninsu matukar bai saba wa Allah mahalicci ba.

Bayan idar da sallah ne sai aka gudanar da addu’o’i na musamman ga Kasa da Jihar Kaduna da kuma Lardin Zazzau.

Dabo FM ta zanta da wasu iyayen kasa a masarautar Zazzau, Alhaji Sani Mahmud Sha’aban Dan Buran Zazzau, ya gode ma Allah da ya sake nunawa al’ummar musulmi irin wannan rana, duk da a bana Idin ya riski wani yanayi na annobar Covid-19. Kuma ya yi addu’an sake ganin wasu shekarun a gaba cikin koshin lafiya da aminci.

Dan Buran Zazzau, ya kuma yi tsokaci kan halin da Najeriya  ke ciki na yanayin katutun bashi da gwamanatoci a kowanne mataki ke ciyowa, inda ya ce akwai babbar kalubale a gaban Najeriya a watanni masu zuwa.
Kuma ya hori shugabanni su ji tsoron Allah da sanya kishin kasa da al’ummar ta gaba fiye da komai. Ya ce matukar aka samu haka, tabbas Najeriya za ta samu mafita.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog