Mun kashe miliyan 523 don ciyar ‘yan makaranta lokacin dokar kulle – Sadiya Faruk

dakikun karantawa
Sadiya Umar Faruk
Sadiya Umar Faruk- Ministar ma'aikatar ayyukan Jinkai da bala'i

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ta kashe Naira miliyan 523.3 domin ciyar da yara ‘yan makaranta a lokacin dokar kulle ta Koronabairas.

Ministar ma’aikatar ayyukan jinkai da bala’i, Hajiya Sadiya Umar Faruk ce ta bayyana haka ranar Litinin a taron gabatar da jawabai da kwamitin yaki da Koronabairas ya saba gudanarwa a Abuja.

Minsitar ta ce tayi jawabin ne domin kore jita-jita da yake yadawa a kan shirin ciyarwar da gwamnatin tarayya take yi.

Ta ce an yi wa tsarin kwaskwarima inda aka fara aiwatar da sabon tsarin a jihohi 3 daga ranar 26 ga watan Maris.

Bisa ga tsarin, ta ce sun tattauna da gwamnoni domin fito da tsarin ciyar da yaran, inda gwamnonin suka amince da a yi tsarin ciyarwa har gida.

“Hubbasar gwamnatin tarayya ce da gwamnatin jihohi na kai abincin har gida.”

“Masu ruwa da tsaki sun fitar da tsarin fara rabon da Lagos, Ogun da birnin tarayyar Abuja.”

Ta ce a Abuja, gida 29,609 ne suka amfana sai Lagos gida 37,589 yayin da gida 60,391 suka ci gajiyar shirin a jihar Ogun daga ranar 14 ga watan Mayu zuwa ranar 6 ga watan Yuli.

Ta kara da cewa hukumar kidudduga ta Najeriya NBS da babban bankin Najeriya sun fitar da kiduddugar addani magidanta da ‘ya’yansu.

“Kiduddugar ta nuna cewa a yawancin gidajen masu matsakaicin karfi akwai mutane 5 zuwa 6 wadanda ana samun 3 zuwa 4 da suke dogara da abin da aka basu a gida.”

“Don haka aka kaddara cewa kowanne gida akwai yara 3.”

“Kowanne yaro yana cin abincin N70”

“Duk yaro daya yana cin abincin N1,400 a kowane kwana 20 da ake zuwa makaranta a wata.”

Ta ce kowanne gida da yara 3 suna cin abincin N4,200 a kowanne wata.

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog