Unguwar Fagge ta koma Kantin Kwari
Bincike Labarai

Yadda unguwar Fagge a Kano ta zama sabuwar Kasuwar Kanti Kwari da Kofar Wambai

Sakamakon dokar kulle da take wakana a jihar Kano, al’ummar unguwannin a cikin jihar Kano musamman wadanda suke kusa da kasuwanni sun koka kan yadda aka mayar da su sabbin kasuwanni bisa rashin bude manyan kasuwanni.

Idan ba a manta ba, gwamnatin jihar Kano ta sanya Litinin da Alhamis a matsayin ranakun da al’umma zasu fito daga 6 na safe zuwa karfe 4 na yamma domin yin siyayya.

Sai dai ba dukkanin kasuwannin jihar gwamnatin ta amince a bude ba.

Yadda Unguwar Fagge ta kasance a yau Litinin

DABO FM ta shaida yadda kwaryar unguwar Fagge da ake kira ‘Cikin Fagge’ ya maye gurbin Kasuwar Kantin Kwari da Kofar Wambai sakamakon rashin bude .

A bayanan da DABO FM ta tattara ta kuma shaida, mafi  yawan ‘yan kasuwanni guda biyu da ke da shagunan ajiyar kaya, su ne ke shiga kasuwar su dauko kayyakinsu, su kuma kasa su a cikin unguwar.

A zantawarmu da wani mazaunin unguwar ya bayyana cewar; “Wallahi kofar gidanmu yanzu a layin Kabobo, cike yake da ‘yan kasuwa, duk sun baza kayyakinsu suna cin kasuwa saboda rashin bari a bude kasuwar da gwamnati ta yi.”

Haka zalika shi ma wani mazaunin unguwar a bangaren da ke kusa da kasuwar Kwari ya shaida mana cewar; “Gaskiya sati mai zuwa zan zagaye kofar gidanmu, duk mai son ya siyar da kaya a wajen sai ya biya N250,000.”

Al’amarin da ya kai a wuraren unguwar na mazabar Fagge A, B da C da yake mafi kusa da Kasuwar Kwari irinsu sashin Plaza, Dandali, Gadar Mahaukaci, Layin Danwawu da sauran guraren, sun cika da ‘yan Kasuwar Kantin Kwari.

Inda a wurare mafi kusa da kasuwar Kofar Wambai, bangaren Fagge D1 da D2 ya cika da ‘yan kasuwar.

Cikowar jama’ar ka iya zama barazana ga mutanen da ke rayuwa a cikin kwarai Fagge sakamakon rashin bin ka’i’dojin hukumomin lafiya na bayar da tazara yayin mu’amalar dole tare da sanya takunkumin fuska. Hakan ya sa wasu ke kallon unguwar za ta iya zama wata cibiya ta masu dauke da cutar ta Kwabid-19.

Layin Kamfala a unguwar Fagge D1 bayan an gama cin kasuwar yau Litinin, 11/06/2020~ 18/09/1442

Masu Alaka

Ganduje ya sassauta dokar hana fita a Kano

Dabo Online

Koronabairas ta hallaka mutum na farko a jihar Kano

Dabo Online

Likitoci guda 10 a Kano sun kamu da cutar Kwabid-19

Dabo Online

Ganduje ya bayar da umarnin dinka takunkumin kariya miliyan 1

Dangalan Muhammad Aliyu

Bude gidajen kallon kwallon kafa da Ganduje ya yi a Kano ya bar baya da ƙura

Dabo Online

Yanzu-yanzu: Mutane 12 sun sake kamuwa da Kwabid-19 a Kano, jumilla 21

Dabo Online
UA-131299779-2