0
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana kara tsawaita dokar hana fita a jihar.
Sanarwar da kwamishinan yada labaran jihar, Muhammad Garba ya fitar, tace gwamnatin ta kara dokar na tsawon mako guda.
Gwamnatin tace ta yanke tsawaita dokar ne bayan tattaunawa gwamnatin tarayya, mahukunta da masana lafiya wadanda suka bayar da shawarar karin, wanda ya cewarta hakan zai kara dakile yaduwar cutar ta Kwabid.
DABO FM ta tattara cewar zuwa yanzu, a ranar Litinin, 11/05/20, mutane 666 ne suka kamu da cutar a jihar Kano, an sallami 66 daga ciki inda mutane 32 suka rasu, kamar yadda ma’aikatar lafiyar jihar ta tabbatar.
