//
Thursday, April 2

Yaki da cin Hanci da Rashawa a Najeriya Siyasa ce da daukar fansa kawai – Farfesa

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Farfesa Egwaikhide Umoudu, babban malami dake koyarwa a Makarantar Koyar da Tsaro ta Najeriya ‘NDA’ dake garin Kaduna, ya bayyana cewa gwamatin Najeriya bata ci nasara a yakin da takeyi na yakar cin hanci da rashawa ba, bisa dalilin cewa dukkan ‘yan Najeriya suna amfani da cin hanci da rashawar.

Malamin ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 29 ga Agusta, 2019, a wani jawabi da yayi a wajen taron Kaddamar da Lakca akan Makarantar ‘NDA’ karo na 10.

Farfesan yace; “Cin Hanci da Rashawa shine yake makalar da cigaban Najeriya. Duk muna amfana da shi. Daukar wanda bai chanchanta aiki ba, shima cin hanci da rashawa ne.

Masu Alaƙa  Kyari ya yi biris da umarnin Buhari na cire wasu Jakadun Najeriya a kasashen waje

“Duk wani dan Najeriya yana yin rashawa, Ilimin mu a lalace yake da rashawa, tsarukanmu a lalace suke da rashawa, har addinanmu ma an cika su da rashawa, dokokin kasar suma a lalace suke da rashawa.”

“Yaki da cin hanci da rashawar ma an siyasantar dashi, ana amfani dashi wajen daukar fansa. Najeriya taci maki 27 bisa 100 a jerin kasashe 180 dake yaki da cin hanci da rashawa.

DABO FM ta rawaito Farfesa Egwaikhide , ya kara da cewa kasar bazata fita daga matsalolin dake damunta ba har sai da karkato da kudaden bangaren Ilimi, saboda Ilimin zai zama gatan kasar a nan gaba.

“Ilimi shine kashin bayan cigaba. Dole yan Najeriya su karka wajen samun Ilimi. Tsarin Ilimin Najeriya cike yake da kura-kurai wadanda suka dakile ingancin karatun kasar baki daya.”

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020