Labarai

A kalla ‘Yan Gudun Hijira 25,000 suka koma Gidajensu na ainahi a jihar Zamfara

Adadin ‘yan gudun Hijira 25,000 ne suka koma gidajensu biyo bayan yunkurin da gwamnan jihar, Bello Matawalle yakeyi na wanzar da zaman lafiya a jihar.

Sakataren hukumar dake bayar da agajin gaggawa na jihar ‘ZEMA’, Alhaji Sunusi Kwatarkwashi ne ya bayyana haka a garin Gusau, ranar Juma’a 30, yayin wata tattaunawarshi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ‘NAN’

DABO FM ta binciko cewa; Kwartarkwashi yace gwamnatin jihar ta kirga mutane 37,000 dake rayuwa a Sansanin ‘Yan gudun hijira biyo bayan addabar jihar da ‘Yan Bindiga sukayi.

Ya kara da cewa tini dai mutane 25,000 suka koma gidajen su na ainahi tare da cigaba da aiwatar da ayyukansu na yau da kullin wadanda suka hada da Noma, Kiwo da sauran su.

Kwatarkwashi yace sauran ‘Yan gudun Hijira guda 12,000 suna jihar Katsina, Kaduna, Kebbi, Sokoto da wani bangaren a jihar Nijar.

Ya bada tabbacin cewa gwamnatin jihar zatayi dukkanin wani kokarinta wajen ganin da maido da sauran mutane zuwa ga dangoginsu cikin aminci da salama.

“Dukkanin ‘yan gudun Hijirar da suke wani waje sunfi son su dawo gida su cigaba da rayuwarsu tare da ‘Yan uwa da abokan arziki.”

Daga cikin wadanda suka samu koma gidajen nasu, Sani Saidu, dan garin Gusami dake karamar hukumar Magaji, ya nuna yabonshi ga gwamnan jihar bisa yunkurinshi na kawo zaman lafiya a jihar.

Karin Labarai

Masu Alaka

‘Yan Bindiga a Zamfara sun kashe shugaban ‘Yan Banga

Akwai yiwuwar INEC ta soke zaben Zamfara bayan ganawar gaggawa da jami’iyyar APC tayi

Dabo Online

Za’a gudanar da Zaben kananan hukumomi ranar 27 a jihar Zamafara

Dangalan Muhammad Aliyu

Zamfara: Jami’an tsaro basa mana aikin komai – Sarkin Shanun Shinkafi

Dangalan Muhammad Aliyu

Jihar Zamfara ta rufe dukkanin iyakokinta don kariyar Coronavirus

Aisha Muhammad

Rikicin Zamfara: Rashin adalci ne ace ban damu da kashe kashen Zamfara ba – Buhari

Dabo Online
UA-131299779-2