Labarai

‘Yan biki sun zama masu karbar ta’aziyyar Amarya bayan ta fada Rijiya a Kano

A garin Gajaja na karamar hukumar Dambatta dake jihar Kano, wata Amarya mai suna Fatima, ta fada rijiya jiya Laraba, kwana daya kafin daurin auren ta.

Sashin Hausa na BBC na bayyana cewa amaryar ta fada Rijiyar ne bisa rashin sani yayin da suka je gidan wankan amarya tare da kawayenta.

Kanin angon marigayiyar ya shaida wa BBC cewa suna tsaye a gidan mawankiyar sai kawai ta zame ta afka cikin rijiyar.

Shi kuwa mahaifin mamaciyar, Alhaji Abubakar ya tabbatarwa da BBC cewa a yau Alhamis aka shirya daura mata aure.

“Auren soyayya ne, ita tana so shi ma yana so. Yanzu haka ma ‘yan biki ne dankam a wurin zaman makoki,” in ji Alhaji Abubakar. 

Ya shaida cewa mawankiyar amaryar ta shiga wani hali kasancewar a gidanta amarya ta fada rijiyar, lamarin da yace suna kokarin shawo kanta domin ko abinci ta kasa kai wa bakinta na salati.

Shima a nashi bangaren, kanin angon, ya bayyana cewa amaryar yar asalin garin Baburan jihar Jigawa ce, tazo garin Dambatta ne duk cikin shirin auren nata.

Shi kuma a nashi bangaren, angon Fadima, bai iya cewa komai ba bisa irin yanayin da yake ciki na dimaucewa.

Karin Labarai

Masu Alaka

Bidiyo: Kalli yacce direbar jirgi wacce ba ta da hannaye take sarrafashi a sararin samaniya

Dabo Online
UA-131299779-2