Babu wani shugaba kuma ‘Janar’ dan damukuradiyya kamar Buhari -Yahaya Bello

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya mayarwa jaridar ThePunch da martani bayan ta zargi Buhari da mulkin kama karya tare da fakewa da damukuradiyya.

Dabo FM ta jiyo Yahaya Bello yana cewa: “Tinda nake ban taba ganin shugaba kamar Buhari ba, a Najeriya ba’a taba ganin shugaban kasa kuma tsohon shugaba a mulkin soja kamar sa ba.”

“Duk mai makala wa Buhari cewa shi shugaban mulkin kama karya ne, to shi yake da raayin mulkin kama karya din.”

Yahaya Bello ya bayyana haka ne a birnin tarayya dake Abuja, kamar yadda DailyNigerian ta rawaito.

Masu Alaƙa  A ƙarshe: Buhari ya rattaba hannun aminta da biyan albashin N30,000

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.