Kotu ta kara baiwa gwamnatin tarayya umarnin sakin Sambo Dasuki

dakikun karantawa

Kotun daukaka kara dake zama a Abuja ta baiwa tsohon mai bada shawara kan harkokin tsaro na kasa, Sambo Daski beli akan kudi Naira miliyan 100.

Haka zalika, kotun ta umurci Sambo Dasuki da ya kawo mutanen da za su tsaya mashi suma a kan kudi Naira miliyan 100 kowannensu.

Sambo Dasuki na a tsare tun shekarar 2015, duk da cewa kotuna da dama sun ba Dasuki beli. A cikin watan Yuli 2018, Ijeoma Ojukwu, wani jojin babbar kotun tarayya a Abuja, ya bayar da beli ga Dasuki akan kudi Naira miliyan 200.

Alkalin ya zayyana sharuddan belin da suka hada kawo mutane da za su tsaya mashi wanda dole su zama ma’aikatan gwamnatin tarayya a mataki na 16.

Amma da kotun daukaka kara ke sake duba batun belin, kotun ta zayyana cewa wadanda za su tsaya mashi dole sai sun kasance mazauna Abuja.

A takardar hukuncin kotun, ta bayyana cewa “Duka wadanda za su tsaya mashi sai sun kawo ma kotu shaidar cewa suna da kadarori a babban birnin tarayya da kudinsu ya kai Naira miliyan 100.”

Kotun ta kara da cewa “Idan akwai bukatar zantawa tsakanin mai kara da wanda ake kara a kan batun zargin, to kada a tsare wanda ake kara, sa’annan a gudanar da zantawar a ranakun aiki kadai tsakanin karfe 9:00 na safe zuwa karfe 6:00 na yamma.”

Ana zargin tsohon mai bada shawarar kan harkokin tsaro da laifin karkatar da kudi da aka ware don yakar ta’addanci, zargin da Sambo Dasuki ya musanta.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog