Labarai

Yan Bindiga sun kone wani Matashi ‘Har Toka’ suka bawa iyayenshi akan sun kasa biyan kudin fansa

A cigaba da kara tsanantuwar ayyukan sace-sace da kashe-kashen mutane, yan Bindiga sun aikata babbar ta’asa akan wani matashi.

Mun samu wani rahoto daga jihar Adamawa cewa; A watannin da suka gabata ne wasu ‘yan Bindiga sukayi garkuwa da wani Matashi mai suna Jamilu Siddiki Liman.

Rahotan ya ja hankulan mutane a shafin sada zumunta na Twitter.

DABO FM ta tattaro cewa yan Bindigar sun kira iyayen matashi kamar yacce suka saba domin yin cinikin kudaden fansar da zasu biya.

Bayan fadar kudaden ne dai, iyayen Jamilu suka bayyana cewa basu da adadin makudan kudaden da ‘yan Bindigar suke bukata.

Rahotan yace; Tin dai daga wannan lokacin, yan Bindigar basu kara kiran Iyayen matashin ba.

A jiya Juma’a, 7 ga wayan Satumbar 2019, ‘yan Bindigar suka kira iyayen matashin, suka ce musu suje su dauki dansu a wajen da suka fada.

Zuwansu ke da wuya suke iske an kone matashi Jamilu har toka inda rahotan yace; Kaya da Takalmin Matashi kawai iyayen suka iya ganewa.

Masu Alaka

‘Yan Bindiga sun hallaka mutane 10 a jihar Katsina

Dabo Online

‘Yan sandan Kano sun cafke mutane 100 da suka shiga jihar don fara ta’asar Garkuwa da Mutane

Dabo Online

Babu inda Boko Haram take da ko taku daya a Najeriya – APC

Muhammad Isma’il Makama

Masu garkuwa da mutane sun kashe turawa a jihar Kaduna

Dabo Online

Da dumi-dumi: Yan bindiga sun afka kan tawagar Sarkin Pataskum, sun kashe ‘yan tawagarshi 3

Dabo Online

Mutum 42 sun rasa rayukansu a harin da ‘Yan Bindiga suka kai wasu kauyukan jihar Zamfara

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2