Kiwon Lafiya Labarai

‘Yan majalissun jiha guda 5 a Gombe sun kamu da cutar Kwabid19

RAJASTHAN: ‘Yan majalissar jiha guda biyar a jihar Gombe sun kamu da cutar Kwabid19, wata majiya ta tabbatar wa da Solacebase.ng.

Solacebase ta rawaito cewar ‘yan majalissun guda biyar suna daga cikin mutum 16 da hukumar NCDC ta fitar cewa sun kamu da cutar a jihar ta Gombe ranar Lahadi.

“Daga cikin majiyoyin namu sun tabbatar mana da cewa guda daga cikin ‘yan majalissun da suka kamu, ya shaida wa wakilnmu cewa daga cikin ‘yan majalissar da suka kamu, akwai masu manyan mukamai a majalissar.”

Kazalika, majiyar ta ce akwai dan majalissar zartarwa na jihar a cikin wadanda cutar ta harba.

Sai dai har yanzu mahutakan jihar basu ce komai game da rahoton ba.

Karin Labarai

UA-131299779-2