Labarai

‘Yan Najeriya 65,000 ne sukayi aikin Hajjin Bana – Hukumar Alhazai

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON, ya bada sanarwar cewa yan Najeriya kimanin 65,000 suke a kasa mai tsarki domin yin aikin Hajji.

Hukumar ta fitar da adadin ne bayan da Alhazan Najeriya suka kammala sauka a kasar a kwanaki kadan da suka gabata.

Hukumar da bayyana haka ne ta hannun jami’inta Dakta Aliyu Tanko, a yayin da yake bayyana manema sanarwar a kasar ta Saudiyya

DABO FM ta tattaro cewa; Ranar Asabar, 10 ga watan Agusta, shine yayi dai dai 9 ga watan karshe na jadawalin watannin Addinin Musulunci.

A duk ranar 9 ga watan Dhul Hajj, ya na kasancewa ranar da Musulmai suke kira da Arfa, inda a ranar ne Alhazai da suke a kasa mai tsarki suke gudanar da aikin Hajjinsu.

Wadanda kuma basu samu damar halartar filin na Arfah ba, addinin Musulunci ya kwadaitar da Azumtar ranar domin samun tagomashi mai tsoka na yafe laifukan shekaru 2. – Kamar yacce Malamai suka bayyana a sharhin Hadisan Manzon Tsira SAW.

Masu Alaka

Hajj2019: Kada jama’a su yadda da kudin aikin Hajjin 2019 da ake turawa a Social Media – Hukumar Alhazai

Dabo Online

Hukumar Alhazai ta rage kudin aikin Hajjin 2019 tare da kara wa’adin biyan kudi

Dabo Online

‘Yan Najeriya 65,000 zasu yi aikin Hajjin 2019, adadin da ya ragu da 10,000 a shekarar 2014

Dabo Online

An samu ragin N51,170 daga cikin Naira miliyan 1.5 na kudin aikin Hajjin 2019 – NAHCON

Dabo Online

Kaduna,Abuja: Kudin aikin Hajji na bana, Naira miliyan 1.5 – Hukumar Alhazai

Dabo Online
UA-131299779-2