‘Yan Najeriya 65,000 zasu yi aikin Hajjin 2019, adadin da ya ragu da 10,000 a shekarar 2014

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON, ya bada sanarwar cewa zuwa yanzu adadin alhazan Najeriya sun kai kimanin 65,000 dake kasar Saudiyya domin sauke farali.

Jami’in hukumar, Dakta Aliyu Tanko ne ya sanarwa da manema labarai a kasar ta Saudiyya. Inda ya kuma bayyana cewa hukumar ta shirya tsaf wajen saukakawa Alhazan yin aiki Hajjin da za’a fara ranar Asabar cikin sauki.

Ya kara da cewa dukkanin alhazan Najeriya suna kasar ta Saudiyya tare da cewa tini dai suka fama yin wasu al’amura da shirin tunkarar aikin Hajjin.

Ya kuma yaba matuka bisa tsarin da hukumomin kasar Saudiyya sukayi domin kaucewa faruwar hadura da matsawa alhazan musamman shirin ranar Arfah da wajen yin jifan Shaidan.

Hukumar ta bayyana cewa ta tanadarwa Alhazan Najeriya wuri na musamman wanda ya hada da titi a wajen jifan Shaidan.

“Mun yaba da tsarin nasu sosai, wannan abin girmamawa ne sosai kuma hakan na nuna cewa akwai kyakkyawar alaka da mutunci dake tsakanin Najeriya da kasar ta Saudi Arabiya.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya rawaito cewa ”Sun tanadi ma’aikatan lafiya guda 350 domin kula da lafiyar Mahajjatan Najeriya.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.