Gwamnan Borno ya baiwa tsofaffin Ma’aikata 10,319 kudadensu na Fansho

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya rattaba hannu kan biyan kudaden barin aiki na ma’aikata 9,898 tare da baiwa iyalan tsofaffin ma’aikata 185 (Wadanda suka mutu) masu ritaya kudin garatuti tare da fara tattaunawa da wasu Iyalan mamatan 236 don biyan nasu hakkin.

A wata takarda da hadimin gwamnan, Isa Gusau ya fitar, ya bayyana cewa tini dai gwamna Zulum ya umarci shugaban ma’aikatan jihar ta ya tabbatar gaggauta sakawa kowa kudaden a cikin asusunsu na Banki.

Ya kara da cewa gwamnan ya sanya hannu don bawa sakatarorin da gwamnan ya tafar yayin ziyarshi ta bazata zuwa babbar sakatariyar Maiduguri, alawus domin karfafa gwiwa.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.