‘Yan Najeriya basu gamsu da jawaban Buhari ba’

Karatun minti 1

Matasan Najeriya a shafukan sada zumunta sun bayyana rashin gamsuwarsu ga jawaban shugaba Muhammadu Buhari.

DABO FM ta tattara cewar a jiya daren jiya Alhamis da karfe 7, Buhari ya yi wa ‘yan Najeriya jawabai a karon farko tin bayan fara zanga-zangar #EndSars tsawon makonni 4.

A wani dan kwarkwaryar bincike da DABO FM ta yi a shafukan sada zumunta sun bayyana yadda al’ummar kasar suke martani ga jawabin shugaban a matsayin ‘Marar Amfani.’

Wasu na ganin shugaban bai yi magana a kan bude wutar da ake zargin jami’an Soji sun yi wa masu zanga-zanga a Lekki dake jihar Legas.

A tsagi guda kuma wasu na ganin bai kamata ace shugaban bai yi magana a kan mutane 20 da ‘yan Bindiga dadi suka harbe a karamar hukumar Talata Mafara ta jihar Zamfara ba.

A cikin jawabin da ya gabatar, shugaba Buhari ya yi kira ga masu zanga-zangar su janye domin a gwamnati ta riga ta amince da kudurori 5 da masu zanga-zangar suka mika wa gwamnati.

Ya kara da cewa tuni shiri yayi nisan don ganin yadda za a kara wa jami’an tsaron Najeriya albashi da walwala.

Shugaban kuma ya ce gwamnatinsa tana nan kan bakarta wajen fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci in da yace ba a taba gwamnatin Najeriya da ta jikan talakawa irin tashi ba.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog