‘Yan Najeriya: Kar ku tsammaci samun tsayayyar wutar lantarki – TCN

Shugaban hukumar rarraba hasken wutar lantarki a Najeriya, ‘TCN’, Usman Muhammad yayi kira ga yan Najeriya da su cire tsammanin samun dauwamammiyar wutar lantarki.

Shugaban ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da Jaridar Punch a ranar Lahadi, Usman Muhammad yace lallai sai an samu hannayen zuba jari sosai a wajen rarraba lantarkin kafin akai ga an samu tsayuwar wutar.

Shugaban yayi misali da nau’ar MCB ta cikin gidaje wacce take kare afkuwar lalacewar wutar gida yayin da wata matsala ta tashi, yace na’urar ce ke tsayar da matsalar wuta a iya inda waya da waya suka hadu ba tare da tafiya ta kona komai na cikin gidan ba.

“Idan na’urar bata iya tsayar da matsalar cikin gida ba, to zata afkawa taransufoma, idan ba’a kare taransufomar ba, to zata afkawa maharbar lantarkin, idan ta gaza samun kariya a maharbar lantarkin, to zata afkawa matattarar lantarkin.

“To wannan shine irin misalin abinda yake faruwa a wajen rarraba wutar lantarkin, shiyasa muka dade muna kiran a zo a zuba hannun jari wajen rarraba wutar lantarkin.”

%d bloggers like this: