Idan har na soki Jonathan, ya zama dole in soki shugaba Buhari – Mal. Idris Bauchi

Mallam Idris Abdulaziz, Bauchi, wanda jami’an DSS suka tsare ya bayyana cewa jami’an tsaron sun kame shi ne bayan sun zargeshi da sukar shugaba Muhammadu Buhari.

Malamin da aka saki ranar Juma’a, ya zanta da wakilin Jaridar Daily Trust, inda ya bayyana cewa jami’an DSS sun fada masa cewa sun kamashi ne bisa sukar shugaba Buhari ne.

“Sun fada min cewa na dade ina zagin shugaban kasa a cikin khudbobi da majalisi na kuma suna da shaidu.”

“Na kalubalance su kunna daya daga cikin audiyon abinda suke zargi na dashi, amma suka gagara kunna ko da guda 1 a matsayin hujjarsu.”

Majiyoyin DaboFM sun tattaro bayan Mallam Idris inda ya bayyana cewa, a kowanne irin matakin gwamnati akayi ba dai dai ba, dole ya fito ya soki gwamnatin kuma don haka dole ya soki shugaba Buhari.

Masu Alaƙa  Mun fitar da 'yan Najeriya miliyan 5 daga kangin talauci da yayi musu katutu - Buhari

“Na fada musu; sukar da nayiwa shugaba Goodluck Jonathan, ban yi kwatankwacinta ga Buhari ba.”

Na fada musu bazan bi son rai inyi shiru idan akayi ba dai dai ba. Yanzu sukar da nakeyi dole ne tafi yawa saboda irin tsanani da ake ciki kuma shugaba Muhammadu Buhari, dan Arewa ne.

Babu adalci, in soki shugaba Jonathan, saboda shi ba musulmi bane kuma in bar shugaba Buhari saboda shi Musulmi ne.


“Ba haka musulunci ya koyar ba. Musulunci yace ayiwa kowa adalci ba tare da duban addini ba.

Kyautatawa ba iya musulmi akeyiwa ba a addinin Musulunci. Musulunci ya koyar damu kyautatawa dabbobi ma ba mutane ba.

Masu Alaƙa  Ko Sheikh Zakzaky zai warke a kasa da kwanaki 1416 da suka ragewa Buhari da El-Rufai?

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: