1
Kungiyar Shi’a ta nesanta kanta daga rahotanni da aka bayyana su a matsayin masu alhaki a kisan mataimakin kwamishinan yan sanda a Abuja.
Shi’a tace, ‘yan sanda da kansu suka kashe jami’in tare da ‘yan Shi’a 11.
A ranar Litinin ne rundunar ‘yan sanda ta bayyana cewa ‘yan kungiyar Shi’a sun harbe DCP Usman Umar a lokacin da suke gudanar da Zanga-zanga a Abuja.
Sai dai mai magana da yawun Shi’, Ibrahim Musa ya nesanta kungiyar da yin amfani da bindigogi.
Yace an farmusu ne a lokacin da suke gudanar da zanga-zangar Lumana.
