Labarai

An kama Malamin makaranta da yayi lalata da Daliba a dakin gwaje-gwaje na ‘Biology’

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta tabbatar da cafke Idowu Daniel, malamin makarantar sakandire mai shekara 28, wanda ake zargi da yin lalata da daliba a wata makarantar kudi dake jihar.

Rahotanni sun bayyana Daniel, malamin wanda yake koyar da kwafuta a makarantar Anatasia Comprehensive ya yi wa dalibar mai shekaru 17 fyade a dakin gwaje gwaje na Biology dake makarantar.

DABO FM ta rawaito cewa a ranar Alhamis, malamin ya cewa dalibai ta biyoshi dakin gwaje-gwajen da littafinta na Kwafuta domin ya saka mata hannu a littafin.

Shigowarta dakin gwaje-gwajen ke da wuya, malamin yazo gabanta tare da shafa mata mama. Rahotannin sun bayyana cewa dalibar ta samu nasarar tsere.

A ranar Juma’a, 28 ga Yuli, majiyoyi sunce Mr Daniel ya kara turawa domin a kirawo masa dalibar tare umarnin ta sake zuwa da littafinta na kwamfuta. “Tana shigowa ne sai ya rufe kofa yayi mata fyade.”

Jaridar Punch ta ce; bayan kwanaki 3 da faruwar lamarin, Mr Daniel ya kara kirawo dalibar cikin dakin gwaje-gwajen tare da bayyana mata cewa batayi kokari a jarrabawar lissafi da Kwamfuta ba.

Sai dai a wannan karon ya bukaci da ta amince ya sadu da ita idan tanaso ya kara mata makin jarrabawar.

Dalibar dai taki amincewa inda ta kuma mika shi gaban shugaban makarantar, daga nan ne aka kai lamarin gaban hukuma.

Tini dai hukumar yan sanda ta bayyana kame Mr Daniel tare da tuhumarshi da aikata fyade.

A nashi bangaren Mr Daniel ya bayyana yaki aminta da zargi da ake masa, ya bayyana cewa “Ban taba wata al’aurarta ba, kawai dai na shafa mamanta ne.”

DABO FM ta binciko Mr Daneil; Ya kara da cewa ya ganta ne a lokacin da take dagawa wasu dalibai maza maman yyin da yake cikin ofishin shugaban makarantar.

Karin Labarai

Masu Alaka

Tsoho mai shekaru 60 ya yi wa Yarinya ‘yar shekara 10 fyade a jihar Imo

Dabo Online

Banyi wa dalibata fyade ba, kawai na shafa mata mama ne – Malami

Dabo Online

Katsina: ‘Yar shekara 14 ta yanke gaban magidancin da yayi yunkurin yi mata fyade

Dangalan Muhammad Aliyu

Mahaifi yayiwa ‘yarshi ciki bayan saduwa da ita sau 3

Dabo Online

An kama malamin Firame da yayi wa dalibinshi mai shekaru 8 ta’adin fyade a Bauchi

Dabo Online
UA-131299779-2