//
Thursday, April 2

Ganduje zai tura kwararru 40 kasar Burtaniya don koyo sana’o’in da zasu koyawa Matasan jihar Kano

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Gwamnatin jihar Kano ta dauko kwararru guda 40 daga fannonin Injiniyanci, Zane-zane da sairan fannoni inda zata turasu kasar Birtaniya don daukar horo.

Gwamnatin tace wadannan kwararru 40 da zata tura kasar Birtaniya, zasu dauko hore ne kuma su dawo jihar domin koyawa matasan jihar Sana’o’i daban daban na dogaro da kai.

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Ganduje ne a bayyyana haka a yayin karbar bakuncin sabbin ma’aikatan hukumar shige da fice da yaye da yayi a ofishinshi.

Dr Nasiru Yusuf Gawuna ne ya wakilci gwamnan yayin ziyarar.

A wata takarda da babban sakataren yada labaran Gawuna, Hassan Musa Fagge ya fitar, ya rawaito mataimakin gwamnan yana cewa; “Babu abinda yafi gina mutane muhimmanci, wannan shine babban dalilin da yasa wannan gwamnatin take ta bada tallafin dogaro da kai.”

Masu Alaƙa  'Yan daba sun kai hari, gidan shugaban APC na jihar Kano

“Za’a gastaka haka idan akayi duba akan cibiyar koyarda da sana’o’i da gwamnati ta kammala, wacce za’a bude ta kwanannan.”Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020