‘Yan Sanda sun kara harbe mutum 2 a jihar Legas

Karatun minti 1

‘Yan sanda a unguwar Oladi, Apapa dake jihar Legas, sun harbe wasu matasan masoya, mace da namiji.

‘Yan sandan sun harbe Mr  Emmaneul Akomafuwa tare da budurwashi Ada Ifeanyi, akan hanyarsu ta dawowa daga kulub din rawa a tsakar daren jiya Asabar.

Jaridar Sahara tace Rahotannin dake fitowa ya bayyana cewa ‘yan sandan sun tare motar Mr Akomafuwa, amma yaki tsayawa, lamarin daya sa dan sandan yayi harbi.

Jaridar tace bayan dan sanda ya harbi Mr Akomafuwa ne budurwar tashi, Ms Ada ta fara yiwa dan sandan ihu da kwakwazo, lamarin daya sa ‘yan sandan suka bata har shashi.

Jaridar ta kara da cewa yanzu haka dai Mr Akomafuwa yana kwance a gadon asibiti domin karbar taimakon gaggawa, inda Ms Ada tace ga garinku nan.

A kwanakin baya ne ‘yan sanda a jihar Legas suka harbe wani matashi maboyin bayan kwallon kafa, Mr Kolade Johnson.

Lamarin daya janyo cece kuce a tsakanin ‘yan Najeriya, musamman ‘yan arewacin kasar inda shugaba Muhammadu Buhari ya nuna rashin jin dadinshi ga kisan Kolade.

Inda a lokaci guda ake zargin shugaban da yin shiru a kan kisan al’ummar Zamfara da akeyi.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Latest from Blog