Labarai

Mabiya addinin Hindu sun yanka Kirista bisa dalilin yanka Saniya a kasar Indiya

Wani Kirista a kasar Indiya ya gamu da ajalinsa bayan da wasu ‘yan addinin Hindu suka far masa bisa yanka Saniya da yayi.

Hukumar ‘yan sandan garin Jharkhand sun s da faruwar al’amarin a ranar Asabar.

‘Yan sandan sunce al’amarin ya faru ne a ranar Alhamis, inda wasu bayyana cewa wasu mutane mabiya addinin Hindu sun afkawa wani dan karamin kauye da mazaunanshi mafi yawansu Kiristoci ne.

Matasan dauke da rodi da wasu makamai sun farwa Kiristocin bayan da suka iske su lokacin da suke fede Saniyar da suka yanka.

Jihar Jharkhand bata daga cikin jihohin da aka  hana yanka ko cin naman Saniya.

Tin bayan darewar mulkin Firaminista Narendra Modi, mabiya addini Hindu suke farwa duk wani wanda suka samu da yin wasa ko yunkurin yanka Saniya.

Jami’iyyar Modi, jami’iyyar ce da ake wa kallon mai ra’ayin rikau na addini Hindu, dalilin haka ne yasa gwamnatin ta kakabawa wasu garuruwa dokar hana yanka ko cin naman saniya.

Gwamnatin Modi tayi yunkurin hana fitar da shanun wasu kasashe tare da hana kowa yankawa ko ci duk da cewa akwai mabiya addinai dayawa da suke cin naman saniyar.

Sai dai Kotun kolin kasar ta dakatar da yunkurin gwamnatin.

Masu Alaka

Jirgin zuwa duniyar Wata na Indiya yayi tutsu, sakanni kadan daya rage sauka a kudancin duniya

Dabo Online

Gwamnatin Indiya ta bayar da hutun wasan ‘Jirgin Leda’

Dabo Online

Yadda Indiyawan Hindu sukayi wanka da cin kashin Saniya don magance Corona Virus

Dabo Online

Bidiyo: Gwamna a Indiya, ta kunyata ma’aikaci akan kashe N2550 ba bisa ka’ida ba

Dabo Online

Zaben2019: Wasu ‘yan Najeriya mazauna kasar Indiya, sun bayyana murnarsu ga nasarar Buhari

Dangalan Muhammad Aliyu

Indiya: An kama dan Najeriya da Hodar Iblis “Cocaine” a kasar Indiya

Dabo Online
UA-131299779-2