Labarai

Kotu ta kwace kujerar Majalissar Tarayya, ta baiwa PDP

Kotun sauraren korafe-korafen zabe dake da zama a jihar Binuwai ta kwace kujerar majalissa tarayya mai wakilcin Oju da Obi daga hannu APGA ta kuma baiwa PDP.

Sashin Hausa na Legit.ng ya rawaito cewa kotu ta tsige dan takarar ne bayan samun INEC da kuskuren lambobi wajen tattara kuri’un zaben.

Alkalin da ya jagoranci shari’ar, Mai shari’a, A.A Adeyele ya bayyana cewa dan takarar PDP, Samson Okwu, shi ne wanda ya lashe zaben da rata ta kuri’a 994 daga kananan hukumomin Oju da Obi.

Kotun ta soke kuri’u 12,994 da jami’an INEC suka rubuta Ogewu ya samu a garin Oju da.” Inda ta bayyana cewa Samson na PDP yana da kuri’a 6,797 a garin.

Kotun ta ce Ogewu na jami’iyyar APGA ya samu kuri’a 754 ne kacal a garin Oju, ba kamar yacce jami’an INEC suka tattara a farko ba.

Kotu ta bada umarnin tsige, David Ogewu, dan majalissa mai wakiltar yanki Oju da Obi, ta kuma baiwa INEC umarnin baiwa dan takarar jami’iyyar PDP takardar shaidar lashe zabe.

Karin Labarai

Masu Alaka

An fara zanga-zangar kifar da gwamnatin Buhari, Jami’an tsaro su kawo dauki -Uzodinma

Muhammad Isma’il Makama

Yanzu-Yanzu: Jiga-jigen APC sun dira a Habuja da duku-duku kan shari’ar zaben Kano

Muhammad Isma’il Makama

Kotun koli ta kori hukuncin kotun daukaka kara, ta tabbatar da gwamnan PDP

Dabo Online

Kotu ta kori karar Abba Kabir Yusuf, ta tabbatar da Ganduje

Dangalan Muhammad Aliyu

Kotun zabe ta kara tabbatar da Dr Ganduje a matsayin gwamnan Kano

Dabo Online

Kotu ta kori karar Dan Majalissar PDP ta tabbatar da APC

Dabo Online
UA-131299779-2