‘Yan Shia sun balle kofar Majalissar Tarayya, sun kori jami’an Tsaro

Kungiyar yan uwa musulmi ta Shia sun balle kofar shiga majalissar tarayyar Najeriya tare da samun damar kore jami’an yan sanda dake gadin wajen.

Yan kungiyar Shia sun fito zanga zangar Lumana domin neman majalissar tarraya ta saka baki ta kuma shiga maganar kamun da akayiwa shugaban kungiya, Sheikh Ibrahim Zakzaky.

Suna gudanar da zanga zanga ne cikin nutsuwa a farko tare da fadar Kalmar “Allahu Akbar” da dai wake wake na nuna rashin goyon bayan gwamnatin Najeriyya bisa bijirewa umarnin kotu na sakar shugabansu Sheikh Zakzaky.

Daga bisani wasu daga cikin yan kungiyar sun hassila, inda suka fara girgide kofar majalissar wanda har takai ga sun balle ta, suka shiga cikin tare da kore jami’an tsaron dake gadin kofar.

Duk da balle kofar da sukayi, jami’an tsaro sun tafi sun barsu inda suke kokari tsare su daga shiga ainahin wajen zaman ‘yan majalissar tarayyar.

Bayan yan kungiyar sun balle kofar ne suka shiga sai suka fara fadin “Free Free Zakzaky.”

%d bloggers like this: