Labarai

Kungiyar ISIS ta dauki alhakin harin Sri Lanka daya kashe mutane 320

Kungiyar ‘Yan ta’addar ISIS tace itace ta gudanar da hari a kasar Sri Lanka, ta fitar da hotunan mayakanta da tace suna su kai hari a ranar Lahadin data gabata.

Harin dai da kungiyar ta kai ya hallaka mutane kimani 320 a ranar bikin murnar Ester a kasar Sri Lanka.

Wannan ne dai hari ne farko da kungiyar ta kai tin bayan da ta samu sabon shugabanci a shekarar 2014.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ta rawaito cewa kungiyar ta fitar da sanarwar daukar alhakin harin tare da bayyana sunaye da hukuma hotunan dakarunta da suka aiwatar da harin a kasar Sri Lanka.

Kungiyar dai ta kira harin da sunan “Hari mai Albarka”

IS, ta fitar da sunayen Abu Obeidah, Abu Baraa da Abu Moukhtar da cewa sune suka kai hari a Otal din Shangri-La,Cinnamon Grand da Kingsbury.

Ta bayyana Abu Hamza, Abu Khalil da Abu Mohammad a matsayin wadanda suka kai harin a Cocina dake garuruwan Colombo, Negombo da Batticaloa.

Abu Abdallah shine cikon na 7, kungiyar tace shine wanda ya kashe jami’an ‘yan sanda 3 a harin Colombo Suburb.

Alkamuna sun nuna harin yana daga cikin hare-haren ta’addanci tin bayan harin 9/11 na kasar Amurka.

Sai da tini dai gwamnatin kasar ta Sri Lanka ya bayyana kungiyar National Thowheeth Jama’ath (NTJ) a matsayin kungiyar da take zargi a hannu a harin

Karin Labarai

Masu Alaka

Anyi yunkurin harba makamai masu linzami a birnin Makkah da Jeddah.

Dabo Online

Babu wani ci gaba da Buhari ya samu a yaki da Boko Haram -Kungiyar Tarayyar Turai

Muhammad Isma’il Makama

Babban Sifetan ‘Yan sandan Sri Lanka ya ajiye aiki bisa mutuwar mutane 320 a harin ta’addanci

Faiza

‘Yan Bindiga sun yanka mai unguwa a jihar Sokoto, sun harbe ‘dan sanda 1

Dabo Online

Subhanallah: Harin ta’addanci a masallacin New Zealand cikin hotuna

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2