Umar Aliyu Fagge
Ra'ayoyi

‘Yan siyasa na amfani da kalmar “Hassada” ko “Bakin ciki” don dakushe masu musu hamayya

Dukkan wani mai ilimi da hangen nesa yana da masaniyar cewa hamayya wani bangare ne daga jikin siyasa ko Gwamnati, ana amfani da adawa a siyasance gurin kawo gyara ko cigaban al’umma, shima wanda yayi wannan adawar kundin tsarin mulkin kasa ne ya halartar mishi yin hakan idan har ba zai ta6a mutunci da muhibbar wanda yake wa adawar ba.

Dalilan da suka halarta siyasa su ne suka halarta hammaya domin inganta sha’anin mulki wanda hakan ne yake banbanta mulkin farar hula da na masu damara.

Amma duk da irin wadannan hujjojin da suka halarta yin adawa ga dukkan mai mulkin al’umma, wasu ‘yan siyasar tare da masu yi musu banbadamnci suna kokarin haramta yin adawar siyasa musamman idan wanda ake yiwa adawar yayi dai-dai da ra’ayin su.

Da zarar mutumin da ake mulka ko wakilta ya nuna gazawar wanda yake mulkarshi, sai kaji sun kada baki suna cewa wannan ai “Hassada” ce ko “Bakin ciki” kake yiwa wannan wakili ko mai mulkar al’umma, ba tare da sanin cewa kansu suke dabawa wuka ba domin kafin wanda suke goyon baya ya samu damar mulka ko wakiltar al’umma’ shima sai da yayi wa mutumin da yake kan mukamin a wancan lokacin. Kaga duk mai fadin hakan ya jahilci kalmar adawa a siyasance kuma shi da mutumin da yake goyon baya su ne manyan yan hassada da bakin ciki.

Babu yadda za’ayi kayi wa mutum adawa a lokacin da kake neman irin mukamin da yake kai, sannan kayi tunanin kai ba za’ayi maka irin wannan adawar ba idan kayi nasara.

Wannan wauta ce da rashin fahimtar mecece siyasa kuma babu wani mahalukin da zai hana alummma fadin ra’ayinsu dangane da wakilcin da ake musu, hanya daya da za’a rage kaifin adawa shi ne ayi wa al’umma abin da ya dace dasu ba abin da aka ga dama ba.

A duk lokacin da wani baragurbin dan siyasa yace kana yi masa hassada ko bakin ciki, to ka tambaye shi meye ma’aunin hassada da bakin ciki a siyasance? A nan ne zaka gane da dan tumasancin siyasa kake magana wanda bai san ma’anar siyasa ba kuma bai san a inane ake samun hassada da bakin ciki ba, domin idan har ka yarda cewa yin hamayyar siyasa bakin ciki ne to tabbas wanda kake kokarin karewa a siyasance babban dan bakin ciki da hassada ne domin watakIla yayi takara da wani kafin yayi nasara a kowane matakin siyasa.

Mu a fahimtar da muka yiwa siyasa kuma take tafiya a kai babu hassada ko bakin ciki a siyasa domin kana so ko baka so, wataran sai ka bar mukamin da kake kai, kaga kenan jahiltar kai ne wani yace anayiwa wani dan siyasa bakin ciki alhalin yasan cewa dama ce ta dan wani lokaci wacce dole ya bar wannan kujerar idan lokaci yayi.

Zamu cigaba da fadin gaskiya a duk inda muka hango baraka daga bangaren masu mulki ko wakiltar mu, su kuma sojojin banbadanci su cigaba da nuna wa duniya matsayin su ta hanyar kiran mutane da ‘yan hassada ko bakin ciki saboda kawai anyiwa wani dan siyasa raddi akan ha’intar al’ummar da suka bashi aikin yi. Muna da kyakyawan zato a gurin dukkan mai bibiyar rubutun mu cewa muna kokarin kamanta gaskiya ba tare da nuna son rai ko bangaranci ba, domin muna da masaniyar cewa babu wani mahalukin dan Adam mara tabbas da zai yi maka abin da Allah bai tsara maka ba a rayuwa. Suma sauran da suke kare karya ta hanya tumasanci da bara muna addu’ar Allah ya ganar dasu.

Rattabawa: Umar Aliyu Musa [email protected]

18/11/2019 09:00 a.m

Karin Labarai

Masu Alaka

#JusticeForKano9: Shirun ‘Yan Arewa da Malaman ‘Social Media’ akan mayarda Yaran Kano 9 Arna

Dabo Online

Romon Dimokradiyya: Kura da shan bugu Kato da kwace kudi, Daga Umar Aliyu Fagge

Dabo Online

#Xenophobia: Abin kunya ne shugaba Buhari ya ziyarci kasar Afirika ta Kudu – Usman Kabara

Dabo Online

Shugabanci ne matsalar Najeriya da Arewa, Daga Umar Aliyu Fagge

Dabo Online

Ra’ayoyi: ‘Rundunar ‘Shege-ka-fasa’ bata lokaci ne’

Hassan M. Ringim

Ko faduwar Atiku zata zama tashin Kwankwaso?

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2